Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da bude makarantar sakandare ta gwamnati da ke Bara a karamar hukumar Gulani bayan shafe sama da shekaru 12 tana rufe sakamakon ayyukan ‘yan tada kayar baya.
Makarantar tare da makarantun gwamnati na Goniri da Babbangida suna aiki ne daga wani wuri na wucin gadi a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Damaturu, tun 2012.
Sabon shugaban makarantar, Mista Sulaiman Tamali, ya bayyana haka a Bara ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci shugaban karamar hukumar Gulani, Dayyabu Njibulwa.