Ƴan bindiga sun ƙona buhunan masara 50 tare da jin ajalin mutane 7 a kauyen Bangi da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja
Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wadanda abin ya rutsa suna a kan hanyarsu ta dawowa da kwasar amfanin gona da suka girbe a gonakinsu
Maharan sun boye a cikin gonar suka jira har sai da manoman suka gama loda buhunan masara 50 a cikin motar kuma shirin komawa gida sai suka bude musu wuta.