FBI ta Amurka ta kama wani shugaban karamar hukuma a Nijeriya kan zargin badakalar $3.3M
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta cafke zababben shugaban karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra, Franklin Ikechukwu Nwadialo, a lokacin da ya isa filin jirgin sama a jihar Texas ta Amurka.
An kama Nwadialo ne bisa tuhumar da ake yi masa kan zargin badakalar kudaden da suka kai kimanin dala miliyan $3.3m
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta fitar, ta ce Nwadialo na fuskantar tuhume-tuhume 14 kuma zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 idan aka same shi da laifi.
Ana zargin Nwadialo da amfani da shafukan zamani irin su; Match da Zoosk da ke kulla soyayya ga yan mata da samari inda ya rika amfani da shi yana damfarar abokan soya
yyarsa.