Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Dokta Wunmi Bewaji, ya nemi Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake tankade da rairaye a majalissar Ministocinsa
Bewaji ya ce har yanzu akwai ministocin da ba su kwazo a ma'aikatun da suke jagoranta don haka ya dace a ce shugaban ya sake duba haka.
A cikin watan Oktoba ne dai shugaban na Nijeriya ya kori wasu 5 daga cikin ministocinsa tare da nada 7 suka maye gurbi
nsu.