Adadin masu fama da ciwon suga a Afrika zai iya haura mutune miliyan 54 nan da shekara ta 2045 - WHO
Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya a yankin Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ya ce adadin masu fama da ciwon suga a nahiyar Afirka zai iya haura miliyan 54 nan da shekara ta 2045 idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
Daraktan na WHO ya ce fiye da mutum milyan 24 ne a halin yanzu suke fama da ciwon suga.
Dr Matshidiso ya ce cutar suga a Afirka na kara kama mutane saboda rashin cin abinci mai kyau, da rashin motsa jiki, da dai sauran su.