Zan iya rantsuwa da Alkur'ani ban saci dukiyar al'umma ba - ElRufa'i

 Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Naziru El-rufa'i ya ce ya shiga siyasa ne kawai don ya hidimta wa al'umma.


Tsohon Gwamnan ya kara da cewa ya tsunduma siyasa ne ba domin ya samu kudi ko satar dukiyar al'umma ba.


Malam El-rufa'i ya fadi haka ne a cikin wani shirin da Gidan rediyon Freedom Kaduna ya watsa da safiyar Talatar nan kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.


A cikin shirin, Tsohon Gwamnan Malam Nasir El-rufa'i ya ce ya wadatu da abin da Allah Ya hore masa tun kafin ya zama Gwamna.


Malam El-Rufai ya ci gaba da cewa a shirye yake ya rantse da Al-Qur’ani a duk lokacin da tsofaffin gwamnonin jihae da na yanzu suka yi haka na tabbatar da cewa ba su taba karkatar da dukiyar al’umma ba.


Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tuhumi gwamnatin Naziru El-rufa'i da karkatar da sama da Naira biliyan 423 cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki.


Tsohon gwamnan da na kusa da shi da aka tuhuma, sun musanta wadannan zarge-zargen, inda suka ce majalisar da gwamnatin jihar ne suke


farautar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp