Za a yi amfani da jiragen soji wajen bai wa masu gyaran lantarkin Arewa kariya-Abdulaziz Abdulaziz

 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu


Tun bayan da Shugaban Tinubu ya nuna fushinsa kan yadda rashin wuta ya addabi yankin Arewa har ya bayar da Umarnin Kan-ta-kwana kan a mayar da wutar, bangarorin da abin ya shafa sun dauki haramar magance matsalar


A wata hira da ya yi da kafar labarai ta DCL Hausa, mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkar yada labarai AbdulAziz AbdulAziz ya bayyana yanda ministan harkokin wutar lantarki ya katse wata ziyarar aiki da yake yi a kasashen waje don amsa kiran shugaban kasa kan ya dawo gida ya dauki aikin gyaran wutar rigi-rigi.


Shi ma Mai bai wa Kasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu tuni ya dukufa, kan umarnin gaugawa da Shugaba Tinubu ya ba shi na samar wa Injiniyoyin gyaran wutan tsaro, inda akan haka ne a yau babban Ministan Tsaron ya biyo sahun sauran wadanda abin ya shafa, wajen bai wa   Shugaban rundunar tsaron Kasa Manjo Janar Kiristofa Musa Umarnin ya gaggauta samar da tsaro ga yankin Shiroro-Kaduna, inda tashoshin da ke bai wa Arewa  harsken lantarki mafi tsoka.


Idan dai ba a manta ba, yankin na Arewa ya shiga duhu na kusan sati biyu sakamakon lalacewar babbar tashar samar da wutar lantarki ga yankin wanda ake zargin 'yan ta'adda ne suka ragargaza ta. Lamarin da ya janyo durkushewar kasuwanci, kiwon lafiya, da kuma walwalar jama'a a jihohi tara da abin ya shafa


A yanzu da Jami'an tsaro suka fara yi wa yankin kawanya, ana sa ran dawowar wutar kasa da sati daya inji kakakin fadar shugaban kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp