'Yan sanda na bincike Mbappe kan zargin keta haddin wata budurwa a Sweden


'Yan sandan Sweden na zargin Kylian Mbappe da keta haddin wata yarinya bayan wata ziyara da ya kai Stockholm, babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan ikirarin da Mbappe ya yi na cewa yana bin tsohon kulob dinsa na PSG bashin kudin da suka kai Dala milyan 60.

Dan kasar Faransa, Mbappe ya ce labarin zargin ya keta haddin wata yarinya ba gaskiya bane kuma karda-kanzon-kurege, an yi ne kawai don a kawar da hankalin mutane game da bashin da yake bi.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani labari da jaridar Punch ta wallafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp