A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sadiq Aliyu Abubakar ya fitar, ta ce labarin ba gaskiya bane, an kirkiro shi ne domin a jefa tsoro da razani a zukatan al'umma.
Sanarwar ta ce yadda lamarin ya faru shi ne, wasu barayin daji dauke da muggan makamai ciki hada bindiga samfurin AK-47 suka yi yunkurin kai farmaki ga wadansu manoma da ke kokarin girbe amfanin gonakinsu, amma 'yan sanda da sojoji da jami'an sa kai na Community Watch Corp suka yi taron dangi suka tarwatsa wadannan barayin daji.
Jaridar Punch da yammacin Juma'ar nan, ta rawaito cewa 'yan bindiga sun far wa wasu mutane da ke sallar Juma'a a kauyen Dan'Ali na karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Sai dai jaridar ba ta ba da cikakken bayanin ko mutane nawa ne suka jikkata ko aka kashe a yayin harin ba.