‘Yan Nijeriya sun gaji da halin matsin rayuwa – Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce da halin matsi da ake ciki a Nijeriya, ‘yan kasar za su yunkuro don kawo sauyi a 2027.


Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Kano.


Kwankwaso ya tarbi ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka daga kananan hukumomin Dala, Kiru da Gwale a gidansa da ke Miller Road a Kano.


Ya ce 'yan Nijeriya musamman ’yan Arewa sun sha wahala sosai a wannan lokacin kuma babu wani da zai tsorata su da zai sa su canja ra’ayinsu.


A cewar sa ya kamata ‘yan Nijeriya su sake tunani, yanzu ta bayyana a fili cewa al'umma na shan wahala a gwamnatin APC kuma ba za su gyara ba.


Ya kara da cewa ko da shirin su na amfani da jami’an tsaro da INEC a zabe mai zuwa, hakan ba zai yiwu ba saboda ‘yan Nijeriya sun gaji kuma tabbas za su yi fafutukar kawo sauyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp