Darakta Janar na hukumar kula da gasanni ta jihar Cross Rivers Lottery and Gaming Agency, Michael Eja, ya bayyana cewa a cikin jimillar al'ummar Nijeriya, an kiyasta akalla 'yan kasar miliyan 60 ne ke shiga harkar caca a kullum.
A cewar Eja, sana’ar caca a Nijeriya na samun bunkasuwa, kuma a halin yanzu ana samun ci gaba tsakanin kudin da ake zubawa N500bn zuwa N600bn.
Eja ya yi magana ne a wajen kaddamar da wani sabon dandalin fara caca, mai suna Woskybet, a Abuja kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.