![]() |
Shugaba Tinubu/Villa |
Majalisar Wakilai ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi magana kan karya doka da ake zarginsa da yi nadin da ya yi a hukumar raya yankin Arewa maso Yamma NWDC.
Hakan ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Isah Muhammad Anka ya gabatar wanda dan majalisa Ayokunle Isiaka ya goyi bayansa a ya yin zaman majalissar na ranar Laraba.
Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce dokar da ta kafa hukumar ta ba da umarni ga kundin tsarin mulkin hukumar ta kula da ayyukanta.
A cewar dokar kowace jiha da ke yankin tana da wakilci a hukumar tare da wakilcin hukumomin tsaro.
Dan majalisa Anka ya ce,shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen wadanda aka nada ga majalisar dattawa domin tabbatar da su a matsayin mambobin hukumar gudanarwa ta NWDC.
Ya ce nadin da aka yi a hukumar gudanarwar NWDC ba a bi ka’idar doka ba, musamman ma ka’idar wakilcin jihohi daidai da wakilci daga manyan hukumomin tsaro.
Ya yi zargin cewa akwai wakilai da yawa daga wasu jihohin yayin da dokar ta tanadi cewa kowace jiha daga Arewa maso Yamma dole ne ta sami wakili daya a hukumar gudanarwar.
Dan majalisar, ya ce jihohin Jigawa da Kano, kowannensu yana da wakilai biyu wanda hakan ya saba wa dokar.
A cewarsa, an samu sabani karara wajen nadin Manajan Darakta na hukumar saboda dokar ta bayyana yadda za a bayar da mukamin wanda za a fara daga Jigawa sai Kaduna, ba jihar Kano ba.
Dangane da rashin wakilan tsaro, ya ce dokar ta bukaci a nada wakilai daga rundunar sojojin Nijeriya da na ‘yan sanda a hukumar. Ba a yi wadannan nade-nade ba, wanda hakan ya haifar da gagarumin gibi a fannin tsaro.