Wutar lantarki ta fi arha a Nijeriya fiye da kasar Senegal, in ji kamfanin TCN




Kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya TCN ya ce duk da karin kudin lantarki da aka samu, amma kasar ta fi wasu kasashe makwabtanta sauki da arha wajen biyan kudin wutar lantarki.

Manajan Daraktan kamfanin Sule Abdul'aziz ya sanar da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Ya ce farashin da 'yan Nijeriya ke biya na kudin wutar lantarki ba tsada bace, kawai dai yanayin samar da wutar ne ke da aiki babba, musamman batun canjin Dala da sauran kudaden kasashen waje.

Ya ce idan aka kwatanta da kasashe irinsu Nijar, Mali, Togo da Senegal, za a ga cewa 'yan Nijeriya kukan-dadi suke yi kan batun farashin wutar lantarki.

Sule Abdul'aziz ya ba da tabbacin cewa 'yan Nijeriya za su iya samun tsayayyiya kuma wadatacciyar wutar lantarki nan da shekaru 5 masu zuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp