![]() |
Gwamnan Jihar sokoto Ahmad Aliyu |
Mazauna jihar Sokoto, musamman wadanda ke cikin babban birnin jihar, sun bukaci gwamnatin jihar da ta sanar dasu wuraren sayar da shinkafar da take sayar wa al'umma.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya kaddamar da sayar da shinkafa ga al’ummar jihar kimanin makonni biyu da suka gabata akan rangwamen kashi 55 cikin dari a garin Kware dake karamar hukumar Kware.
Wannan mataki a cewar gwamnan na daga cikin wani mataki na saukaka rayuwa ga jama’a musamman ma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Gwamnan a yayin kaddamar da sayar da shinkafar kimanin makonni biyu da suka gabata ya ce, za a sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 a kan kudi N38,700, yayin da 25kg za a sayar akan N19,350 kuma ana sa ran za a sayar da 10kg akan farashi, naira 7,740.
Gwamnatin jihar ta kashe kudi naira biliyan 14.488 domin sayen shinkafar tare da tireloli 280.
Wani mazaunin birnin sokoto Malam Usman Bello,ya ce dadewar da akai ba a sayar da shinkafar ba a hankali yana kara ruguza al’ummar jihar.
Ya ce jama’a da dama a jihar sun sanya rai da sayar da shinkafar sosai, ya kara da cewa sun dade suna jira tun lokacin da aka kaddamar da sayar da abincin amma abin takaici, da alama babu batun sayar da shinkafar