Talauci da rashin aikin yi ne ke haddasa matsalar rashin tsaro a Arewa –Abdussalami Abubakar

Abdussalami Abubakar 


Tsohon shugaban mulkin soji, Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Arewacin Nijeriya na faruwa ne sakamakon talauci, rashin aikin yi da gazawar hukumomi.

Tsohon shugaban ya bayyana cewa wadannan  abubuwa sun ta ka muhimmiyar rawa wajen rashin tsaro, tare da yin illa ga kasar nan.

Abdussalami Abubakar ya bayyana haka ne a Alhamis dinnan ya yin wata lakca da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya shirya.

Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da kada su karaya wajen yaki da rashin tsaro, yana mai jaddada cewa yaki da rashin tsaro alhakin kowane mutum ne dake cikin kasar.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su hada kai da gwamnati da hukumomin tsaro domin magance matsalar rashin tsaron.

Ya kara da cewa tushen matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin Arewa, da sauran matsaltsalu,ya faru ne saboda tsananin talauci da rashin aikin yi, da yaduwar kananan makamai da kuma gazawar gwamnati.

A cewar tsohon shugaban waɗannan abubuwan sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar rashin tsaro,dole sai kowa ya tashi tsaye domin hakki ne ga al'ummar kasar baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp