Fitacen dan siyasar na Nijar da yake madugun adawa zamanin mulkin farar hula Hama Amadou ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Hama Amadou na daga cikin fitattun 'yan siyasar Nijar da suka yi suna a kasar.
Daga cikin mukaman da ya rike a lokacin yana raye hada na Firaminista a lokacin gwamnatin marigayi Tanja Mamadou da kuma mukamin shugaban majalisar dokoki a lokacin gwamnatin Issoufou Mahamadou.