Bola Ahmed Tinubu/Joe Biden |
Tattaunawar ta wayar tarho da ta gudana da misalin karfe 4 na yamma agogon Nijeriya, a ranar Talatar nan, wadda aka shafe kusan mintuna 30 suna tattaunawa.
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.Tuggar ya ce,kiran ya shafi hadin gwiwa ne a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban ya kuma godewa Amurka bisa hadin gwiwa a fannoni da dama da suka shafi fannin tsaro a Afirka da yammacin Afirka baki daya.