Shugaba Tinubu a shirye yake ya samar duk abin da ake bukata don kawo karshen matsalar tsaro – Ministan Tsaro


Ministan tsaro Badaru Abubakar


Ministan tsaro, Badaru Abubakar, ya umurci sojoji na 17 Brigade Katsina da su kawo karshen matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar Katsina, yana mai cewa shugaba Bola Tinubu a shirye yake ya samar da duk wani abu da ake bukata domin kawar da rashin tsaro. 


Ministan ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a garin Gurbin Baure da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga sojojin a birged 17.



Tun da farko, Badaru Abubakar ya shaida wa sojojin cewa shugaba Bola Tinubu ya ji dadin ci gaban da sojojin suka samu wajen yaki da ‘yan fashin daji a cikin ‘yan watannin da suka gabata,a cewar sa shugaba Bola Tinubu ya amince da ci gaban da ake samu wajen yaki da ‘yan fashin daji a jihar.


Ministan da yake zantawa da manema labarai ya ce a ‘yan watannin da suka gabata ana samun ci gaba a kowace rana, kuma ya yi imanin cewa dukkan jihohin kasar na bayar da hadin kai wajen kawo karshen ‘yan fashin daji a yankin Arewa maso Yamma,inda yace ma'aikatar tsaro na bukatar tallafi da yawa daga al'umma.


Ya ce hanyar Zariya zuwa Gusau ta yi kaurin suna wajen masu garkuwa da mutane,amma jami'an tsaro suna aiki tukuru kuma ya gamsu da irin kokarin da su ke wajen kawo karshen hare-haren da masu ababen hawa ke fuskanta a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp