Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman, ya ce sabon tsarin karatu na makarantun firamare zai fara aiki a duk fadin kasar daga watan Janairun 2025.
Da yake gabatar da jawabin sa a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja a ranar Litinin,FarfesaTahir Mamman ya bayyana cewa a sabon tsarin karatun, za a bukaci daliban da ke makarantun Firamare da na sakandare su laƙanci akalla sana’o’i biyu.
Ya ce, yana da kyau sosai dalibai su sami damar kammala makaranta da aƙalla ƙwarewa kan ayyukan hannu biyu domin samun rayuwa mai inganci.
Ya Kara da cewa wannan wajibi ne da ya shafi dukkan makarantu a Najeriya, na gwamnati da masu zaman kansu, kuma duk makarantu za su aiwatar da shi.