Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta kama wani Ango dan shekara 30, mai suna
Motunrayo Olaniyi, bisa zarginsa da daba wa matarsa mai suna Olajumoke ‘yar shekara 25 wuka har lahira.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Asabar a Legas.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1:00 na rana a Amazing Grace Estate, Elepe, a yankin Ikorodu na jihar.