Rundunar sojin Nijeriya za ta dauki karin kananan sojoji


Sai dai rundunar sojin ta gindaya sharudda da za a cika kafin matasan su nema.

Daga cikin sharudda, rundunar sojin ta ce dole ne matasan da za su nema su kasance marasa aure kuma 'yan asalin Nijeriya kuma su mallaki katin shaida na kasa NIN da kuma lambar BVN.

Kazalika, ana bukatar matasan da za su nema su kasance lafiyayyu a jiki da tunani.

Haka kuma ana bukatar dole matasan su kasance ba su taba aikata wani laifi da kotu ta yanke musu hukunci ba.

Sannan ana bukatar matasan da za su nema ya kasance suna da takardar shaidar kammala sakandare kuma ya kasance sun ci darussa 4 ciki hada Turanci.

Sannan matasan su kasance suna da takardar haihuwa daga asibitin gwamnati ko hukumar kidaya ta kasa ko wadda kotu ta amince da ita. Sannan su kasance 'yan shekaru 18-22. Kazalika, tsawonsu ya kasance na maza 1.68 mata kuma 1.65.

Ana shawartar matasan da su je shafin yanar gizo na rundunar sojin don cikewa ta nan ta nan. Kuma ba a biyan ko sisin kobo a yayin cikawar.

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp