Rundunar sojojin Nijeriya ta bai wa Nana-Fatima Bolori, wata hazika yar jihar Borno, tallafin karatu.
Kwamandan Rundunar Joint Task Force, Operation Hadin kai Manjo Janar Wahdi Shuaibu, da ke Arewa maso gabas ne ya sanar da haka a ranar Alhamis a Maimalari Cantonment da ke Maiduguri.
Manjo Shu’aibu ya bayyana cewa tallafin karatun na da nufin karfafa dangantakar sojoji da jama'a da kuma samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar da ya dace.
A cewarsa, tallafin da za a bata zai biya kudin karatun ta wanda zai tallafa mata har ta samu nasarar a rayuwar ta,saboda tallafi a harkar ilimi yana da matukar muhimmanci
Ya kara da cewa wannan yunƙurin ya yi daidai da ra’ayin babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja na tallafa wa marayun da suka yi abin yaba wa da kuma ƙwazo a manyan makarantun gwamnati na Nijeriya.