NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta rage farashin man fetur


Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta rage karin farashin man fetur da tayi a yan kwanakin nan.

Bayanin hakan na a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kwadagon ta NLC ya fitar, Joe Ajaero, a Abuja, yana mai cewa  karin kudin ya kara ta’azzara talauci a duka fadin kasar nan, kuma babu wani fa’ida ta zahiri tattare da shi.

Sabon karin farashin man fetur din ya kai Naira 1,030 kan kowace lita a gidajen mai na kamfanin NNPCL mai kula da harkokin mai a Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp