Tsohon mataimakin shugaban kasa a Nijeriya Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan halin da ya ce dimokuradiyya na ciki a kasar, inda ya yi gargadin cewa kasar na dab da fadawa mulkin kama-karya na jam’iyya daya da ke neman mamaye ko'ina.
Atiku Abubakar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a don bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun 'yancin kai, ya bukaci masu fada a ji a siyasance da su hada kai su kare tsarin dimokradiyya daga fadawa cikin mulkin kama-karya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanayin siyasar kasar na cikin razani, inda ya yi zargin jam'iyya mai mulki ta yi amfani da tsarin cikin gida don raunana jam'iyyun adawa.
Ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu rike da madafun iko da su tashi tsaye wajen kwato dimokradiyya daga halin da ya ce ta shiga na ha'
ula'i.