Manajan Daraktan
kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya Sule Abdul'aziz ya sanar cewa kasar na ba kasashe makwabta na Togo da Benin wutar lantarki ta sa'o'i 24 a duk rana.
Sule Abdul'aziz ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi a wani shirin gidan talabijin na Channels.
Ya kara cewa Nijeriya na samar da lantarkin ga wadannan kasashe kuma suna biya yadda ya kamata.
Sai dai ya ce ko a Nijeriya ma akwai masu samun wutar lantarki ta sa'o'i 24, musamman waɗanda ke saman tsarin Band A, suna samun ta sa'o'i 20-22, kama yadda jaridar Punch ta rawaito.
Kamfanin TCN dai ya ce an tsara ba waɗanda suke saman tsarin Band A, wutar lantarki ta sa'o'i 20-24, sai na saman Band B aka tsara ba su wutar lantarki ta sa'o'i 16-20, sai waɗanda ke saman tsarin Band C aka tsara ba su wutar lantarki ta sa'o'i 16-20 a rana.