Layin wuta |
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito cewa TCN ya ce ma'aikatan su sun gano dalilin da ya haddasa matsalar wutar lantarki a layin Ugwuaji-Apir mai nauyin kilo 330 (kV).
Babban jami'in hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya ce an gano matsalar ne a yankin Igumale da ke Jihar Binuwai, a cewarsa, yankin da aka samu matsalar, an gano yana da karfin 330kv a cikin dajin Igumale da ke jihar Benuwe.
Ya kara da cewa jami'an TCN na aiki tukuru domin shawo kan matsalar wutar lantarki da ta addabi wasu yankunan.