MƊD ta Jajanta wa Nijeriya kan fashewar tankar mai a Jigawa




Wakilin Babban Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da mummunan fashewar wata tankar man fetur a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga watan Oktoba, Simão ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da al'ummar Najeriya.

Fashewar wadda ta afku cikin muni ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 150 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya yi matukar barna.

Simão ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda bala’in ya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp