Wuraren da abin ya shafa sun hada da Ajebamidele, Omisanjana da Atlas duk a Ado Ekiti, Ikere Ekiti, Ise Ekiti da Emure Ekiti.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye unguwannin a karshen makon da ya gabata, ya kawo cikas ga harkokin zirga-zirga, zamantakewa da tattalin arzikin yankin.
Ruwan saman ya yi awon gaba da sandunan turakun lantarki a kusa da Deeper Life Campground a Ajebamidele, unguwar da ke da yawan jama'a a babban birnin jihar.