Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC ya kawo karshen yarjejeniyar sayen mai da matatar Dangote a hukumance, inda ta bude kasuwa ga sauran ‘yan kasuwa su sayi mai kai tsaye daga matatar.
Wannan matakin na nuni da cewa kamfanin na NNPC ba zai cigaba da zama dillali tsakanin matatar da 'yan kasuwa ba, da hakan zai bai ‘yan kasuwa damar tattaunawa kan farashi kai tsaye da matatar Dangote.
Wannan sauyin ya zo daidai da tsarin kasuwanci, inda matatun mai za su iya sayar da man kai tsaye ga 'yan kasuwa a duk lokacin da suka bukata.