Bayanan da jaridar Daily Trust ta rawaito sun nuna cewa a rubu'i na uku na shekarar 2023, masu Otal din, sun yi cinikin Naira bilyan 28.97 kwatankwacin kaso 67%, yayin da a rubu'i na uku na shekarar 2024, suka sanar da yin cinikin Naira bilyan 48.49 kwatankwacin kaso 192%.
Kazalika, masu Otal din sun sanar da samun riba daga Naira bilyan 5.64 a rubu'i na uku na shekarar 2023 zuwa Naira bilyan 16.44 a rubu'i na uku na shekarar 2024.