Masu gidajen mai a Nijeriya sun koka kan rashin samun ciniki sakamakon yadda wasu daga cikin 'yan kasar suka ajiye ababen hawansu
Hakan na zuwa ne sakamakon matsin rayuwa da ake fama da ita a kasar bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi.
A yanzu haka dai farashin litar man fetur ta haura N1,000 yayin da kafin janye tallafin yan kasar ke sayen litar kasa da N200