![]() |
Majalisar wakilai |
Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance yawaitar Hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin Faskari, Kankara, da Sabuwa ta jihar Katsina.
Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan wani kudiri da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Faskari/Kankara/Sabuwa na jihar Katsina, Sanata Shehu Dalhatu Tafoki ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
Da yake gabatar da kudirin, ya nuna damuwarsa kan yawan Hare-haren ‘yan bindiga a mazabar ta sa cikin watanni hudu da suka gabata.
Ya ce, A ranar Juma’a, 4 ga Oktoba, 2024, ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa ‘yan kungiyar sa kai ta Jihar Katsina kwanton bauna, inda suka halaka mutum shida, suka jikkata wasu biyu, tare da kwace musu kayan aiki.
Bayan kwana biyu, a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba, 2024, ‘yan bindigar sun far wa mutanen kauyen Balan Dawa, inda suka kashe uku tare da yin garkuwa da wasu mata. Haka zalika a ranar Litinin, 7 ga Oktoba, 2024, lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari kan hanyar Funtua zuwa Gusau, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba.
Dan majalisa Shehu Alhaji Tafoki ya ce lamarin ya tabarbare har ya zuwa yanzu ‘yan bindigar na bayar da asusun banki domin a basu kudin fansar mutanen da suka dauka,duk da kokarin da hukumomin gwamnati suka yi a baya da tura jami’an tsaro, har yanzu ana ci gaba da yin wannan ta asa a wadannan yankuna, lamarin da ke nuni da cewa dabarun da ake amfani da su a halin yanzu ba su isa ba.
Ya kara da cewa rundunar sojojin Nijeriya da 'yan sandan Nijeriya, duk da abin a yaba musu a kokarin da suka yi a baya, dole ne a yanzu su rubanya kokarin su wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.