Majalisar Dattawan Nijeriya |
A yau ne majalisar dattawa za ta tantance ministocin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika mata domin tantance su.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi bincike tare da wanke wadanda aka nada, gabanin tantance su a yau.
A satin da ya gabata ne dai Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul, inda ya kori ministoci shida tare da nada wasu sabbi bakwai.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar litinin wadanda aka nada sun sun je ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado, domin gabatar da takardunsu.
Sanata Lado, a wata sanarwa da ya fitar, ya tabbatar da cewa, wadanda aka nada a matsayin ministocin, majalisar dattawa, za ta fara tantance su yau a harabar majalisar a Abuja.