Masu Bara a Abuja |
Da suke mayar da martani a ranar laraba, wasu mabarata, masu bukata ta musamman, sun nuna rashin amincewarsu da matakin da aka dauka, inda suka bayyana damuwarsu a lokacin da suka ziyarci babban ofishin Daily Trust a Abuja.
Auwal I. Alhassan, wanda ya yi magana a madadinsu, ya soki mahukunta a birnin tarayya da rashin yin hulda da su, ko kuma magance korafe-korafensu kafin a ba da umarnin korar su.
Ya ce, abin takaici ne mahukuntan su ce sai sun koresu daga inda suke duk da suna da hakkin rayuwa a ko ina.
Ya kara da cewa, baya ga kungiyar SERAP, babu wata kungiya mai zaman kanta, ko kungiyoyin farar hula, ko kungiyoyin addini da suka kai musu dauki.
Alhassan ya yi ikirarin cewa wadanda aka kama suna rayuwa ne a cikin mawuyacin hali a gidan gyaran hali da ke Bwari, ba su da abinci, ruwa, da kuma kula da lafiya.