Lampard zai dawo aikin horas wa bayan sallamar da Chelsea ta yi masa

Frank Lampard


Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Lampard, ya bayyana shirin sa na komawa horas wa bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sallame shi a shekarar 2021.


A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis, Lampard ya kuma bayyana sha'awar jagorantar tawagar kwallon kafa ta Ingila.


Rahotanni sun bayyana cewa, Lampard na daya daga cikin kociyan da ake alakanta shi da karbar tawagar Ingila tun bayan Gareth Southgate ya ajiye aiki bayan kammara Euro 2024.


Ya ce matsayina sa na tsohon dan wasan Ingila wanda ya buga wasa sau 100, ba bu shakka zai iya jagorantar tawagar kasar ta Ingila a matsayin mai horas wa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp