Shugaban tsagen jam’iyyar NNPP na kasa Dr. Gilbert Agbo wanda ya jagoranci gangamin adawa da Kwankwasiyya a sakatariyar jam’iyyar a Minna jihar Neja, ya ce Kwankwaso da tawagar sa ta Kwankwasiyya barazana ce ga ci gaba da wanzuwar jam’iyyar.
Da yake jawabi a wurin taron shiyyar Arewa ta tsakiya a Minna, Dr. Agbo ya jaddada cewa dakatarwar da jam'iyyar ta yiwa Kwankwaso a Legas ya kawo karshen zama mamba da hannun a jam’iyyar nan take.
Dr. Gilbert wanda shi ma ya jagoranci kona jar hular ta kungiyar Kwankwasiyya a sakatariyar jam’iyyar ta jihar a Minna, ya ce matakin ya nuna karara na ballewa daga bangaren Kwankwaso.
Dokta Agbo ya ce ana sa ran gwamna Kabir Yusuf na jihar Kano zai gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar jam’iyyar saboda rashin bin ka’idojin jam’iyyar da kuma daukakar jam’iyyar.