Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta ce tana tausayawa da halin matsi da ake ciki



Kungiyar gwamnonin Nijeriya

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta bayyana tausayawa ga ‘yan kasar saboda halin da ake ciki, inda ta amince da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a Nijeriya, tare da bayyana fatan cewa sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi zai haifar da sakamako mai kyau nan ba da jimawa ba.


Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya bayyana matsayar gwamnonin yayin wata ganawa da manema labarai bayan taron kungiyar NGF a Abuja.


Ya ce cire tallafin man fetur ya kara ta’azzara matsalolin tattalin arziki,tsadar kayayyaki, lamarin da ya sa ‘yan Nijeriya da dama ba sa iya biyan bukatun yau da kullum.


A nasa bangaren gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce kungiyar gwamnonin ta bayyana fatanta na cewa ganawar da suka yi a baya-bayan nan da mukaddashin Darakta Janar na ma’aikatar tsaro  Adeola Ajayi, da kuma ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro zai karfafa hadin gwiwar tsaro a jihohi.


Ya ce sun kuma gana da Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, wanda ya yi musu bayani kan yadda aka cire tallafin mai gaba daya, kalubalen da kamfanin ke fuskanta, da kuma shirinsa na rage radadin radadin da suke fuskanta na hauhawar farashin litar mai na baya-bayan nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp