Kotu ta umurci tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello da ya gurfana a gaban ta

Yahaya Bellon/Tsohon gwamnan jihar Kogi.

Wata babbar kotun tarayya da ke Maitama ta yi sammaci ga tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, inda ta umarce shi da ya gurfana a gaban ta a ranar 24 ga Oktoba, 2024.

Ana tuhumar Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu Umar Oricha da Abdulsalami Hudu a bisa wasu sabbin tuhume tuhume guda 16 da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa zagon kasa ta EFCC ta kai gaban ta.

A baya dai wata kotun karkashin mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da sammacin kama shi a ranar 17 ga watan Afrilu.

Yahaya Bello na fuskantar tuhume tuhume 19 da suka shafi karkatar da kudade da kuma karkatar da naira biliyan 80.2 a gaban kotun mai shari’a Nwite amma ya kasa gurfana a gaban ta.

Mai shari’a Maryanne Anenih, wacce aka shigar da sabbin tuhume tuhumen a gabanta, ta yanke hukunci a ranar Alhamis dinnan cewa, dole ne tsohon gwaman ya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa kan tuhume tuhumen da ake masa.

Sammacin ya biyo bayan bukatar da hukumar EFCC ta shigar gaban ta,hukumar dai ta yi ikirarin cewa Yahaya da wadan da ake tuhuma sun karkatar da kudaden da aka damka musu.

A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Anenih ta umurci hukumar EFCC da ta buga sammacin a cikin wata jarida da ke yaduwa da kuma manna kwafin sammacin a wuraren da ake gani iya gani.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp