Kotu ta ce Hisbah ba ta da hurumin kama Murja Kunya

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 11 karkashin mai shari’a Nasir Saminu ta yanke hukunci kan karar da Murja Ibrahim Kunya ta kai Hukumar Hisbah da Kwamishian Yan Sandan Kano da Asibitin Dawanau da kuma alkalin kotun shari’ar Musulunci ta Kwana Hudu.

Mai shari’a Nasir Saminu ya ce, Hukumar Hisbah ba ta da hurumin kame ko bincike ko gurfanar da wani mutum a Kotu.
Ya ce, aikin Hisbah shi ne wa’azi, amma batun kama mutane da suke yi cushensa aka yi, amma babu shi a doka kamar yadda Freedom Radio, Kano ta rawaito.

Kotun ta kuma yi watsi da gurfanar da Murja da aka yi a Kotun Kwana Hudu inda ta ce hakan ya saba wa doka.

Mai Shari’a ya kuma umarci a gaggauta ba Murja Kunya wayarta da katin cirar kudinta na ATM.

Kotun ta kuma umarci Murja Kunya ta biya 'yan sanda da Asibitin Dawanau Naira Dubu Dari Biyu kowanensu sakamakon ta gaza kawo laifin da suka yi mata a Kotun.

Mai shari’a ya kuma umarci Kwamishinan Yansanda ya kama Murja Kunya idan ta aikata wani laifi na yaɗa abin da ya saɓa wa addini da al’ada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp