Wata babbar kotu a jihar Kano ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano da ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.
Mai shari’a Sanusi Ma’aji na babbar kotun jihar ne ya bayar da umarnin a karar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta shigar a kan jam’iyyar APC da wasu 13 a ranar Juma’a.
A cewar mai shari’a Ma’aji, KANSIEC tana da ikon gudanar da zabukan kananan hukumomi 44 da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.
Mai shari’a Ma’aji ya kuma umurci hukumomin tsaro da su gaggauta bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyi a yayin gudanar da zaben da aka shirya yi a gobe.
Idan za ku tuna a ranar Talata mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano ya dakatar da gudanar da zaben kananan hukumomi.