Ko ku tuba ko mu aike ku zuwa ga mahaliccinku- Matawalle ya gargadi masu fallasa wa ‘yan bindiga bayanai a Nijeriya

 


Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya gargadi ‘yan bindiga da suka addabi kasar nan kan cewa su tuba ko kuma a aike da su zuwa ga mahaliccinsu tare da gargadin masu fallasa wa ‘yan bindiga bayanan sirri.

Ministan ya yi wannan gargadin ne a wata ziyarar aiki da ya kai kauyen Gundumi da ke kananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani jawabi da ya yi a wajen kaddamar da shirin "Operation Fansan Yamma" a ranar Laraba, ministan ya bukaci goyon bayan al'umma domin kawo karshen matsalar tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp