Mahajjata |
Gwamnatin Bangladesh ta rage farashin kudin aikin Hajji a ranar Laraba ga mahajjatan kasar don yin tafiya cikin sauki a lokacin aikin hajji na shekara mai zuwa.
A shekarar da ta gabata, Saudiyya ta bai wa Bangladesh kason maniyyata 127,000, amma hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kudin jirgi da za su je ya sa dubu 85,000 ne kawai suka iya yin tafiyar.
A shekarar 2024, mafi karancin kudin aikin Hajji da gwamnati ta saka ya kai kusan dala 5,000 amma ta ce a shekarar 2025, zai ragu da kusan kashi 20 cikin dari.
Sakataren ma’aikatar kula da harkokin addini,Matiul Islam ya shaida wa Arab News cewa cikin shekara mai zuwa, an samu ragin dala 920,ya ce an samu ragin ne na saboda rage kudin jirgi da wuraren kwana.
A cewar sa mahajjatan za su zauna a wani masauki mai nisan kilomita 3 daga babban masallacin Makkah.Kasar Bangladesh dai, na daya daga cikin kasashen musulmi mafi yawan al’umma a fadin duniya.