Karuwa ta yi ajalin dadironta a Lagos bayan ya dauko ta kwanan-gida


'Yan sanda a Lagos sun sanar da kama wata mata mai zaman kanta da aka fi sani da karuwa bisa zargin daba wa wani mutum mai shekaru 48 wuka ya mutu har lahira a Lagos.

Ana zargin Joy Kelvin ta daba wa Dadiron nata wuka, mai suna Okafor, a gidansa, inda ya ce ga garinku nan.

Abokin marigayin ne ya kai rahoton faruwar lamarin a sashin ‘yan sanda na Ilasan, kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya shaida wa jaridar PREMIUM TIMES.

Wanda ya kai rahoton ga 'yan sanda ya ba da labarin cewa ya samu kiran waya daga wani abokinsa na kut-da-kut cewa karuwar da abokinsu ya kawo kwanan-gida ta daba masa wuka a cikin gidansa da ke rukunin gidaje na Jakande Housing Estate, a unguwar Lekki da ke Lagos.

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp