Mazauna Kano sun yi watsi da sabuwar zanga-zangar da aka fara a wasu sassan kasar, yayin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.
An fara yada zanga-zangar ranar 1 ga Oktoba, 2024, mai taken "FearlessInOctober", a shafukan sada zumunta, wasu watanni biyu bayan zanga-zangar #EndBadGovernance ta Agusta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Da ta ke lura da halin da ake ciki a Kano, Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin da aka ware ranar 1 ga watan Oktoba domin hutu, mutane da dama sun zabi zama a gida.
Duk da haka, wasu sun tafi don gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum.
Manyan tituna sun dan yi shiru babu cunkoson ababen hawa, yayin da aka bude shaguna da sauran kananan sana'o'i.
Binciken gaggawa da aka yi a manyan kasuwanni kamar Kwari, Sabon Gari, Singer da Kurmi ya nuna cewa galibin kasuwannin su ma a bude suke sai dai shaguna ‘yan kalilan da ke a rufe.
Bayanai dai sun ce an fara gudanar da zanga-zangar a biranen Legas
da Abuja.
Wannan gaskiya ne
ReplyDelete