Jam'iyyun siyasa za su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben gwamnan jihar Ondo





Farfesa Mahmood Yakubu


Gabanin zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ‘yan takarar da za su fafata a zaben za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya wanda kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar yake jagoranta.


Kwamitin na da nufin tabbatar da ‘yan takara sun yi alkawarin gudanar da zabe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.


Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin wani taro da kungiyoyin farar hula.Ya ce kwamitin zaman lafiya na kasa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar GFCR, na gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata.


Yakubu ya bayyana muhimmancin gudummawar da kungiyoyin farar hula ke da su, inda ya jaddada rawar da suke takawa wajen inganta zabe cikin kwanciyar hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp