Iyayen masu Zanga-zangar tsadar rayuwa da aka kama a Kano na neman adalci a Majalisar jihar


Majalisar dokokin Kano.



Iyayen matasan da aka kama yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya sun mamaye majalisar dokokin jihar Kano, suna neman a yi musu adalci.


Da yake magana a madadin iyayen matasan Malam Nura Ahmad, ya ce kimanin matasa 70 ne aka kama su aka kai su Abuja, inda ake ci gaba da tsare su.


Ahmad ya nuna damuwarsa kan halin da matasan su ke ciki, inda ya ce tun da aka kama su babu daya daga cikinsu da aka bari ya yi wanka , kuma sau daya ne kawai ake ciyar da su a rana.



A nasa Bangaren shugaban masu rinjaye na majalisar da ya karbi iyayen yaran ya ce suna iya kokarin su wajen ganin sun bi duk matakai da ake bi wajen karbar belin matasan.


Ya yi kira ga ministan shari a da ya shiga maganar domin ganin an bayar da matasan a hannun beli

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp