IPMAN |
Kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya IPMAN, ta sanar da cewa tana ci gaba da tattaunawa da matatar mai ta Dangote kan yadda za su fara sayen mai kai tsaye daga matatar.
Kungiyar ta karyata rahotannin baya bayan nan da ke ikirarin cewa ta zargi Dangote da hana mambobinta sayan mai kai tsaye daga matatar.
A baya dai an ruwaito cewa kamfanin man fetur na kasa NNPCL zai baiwa sauran ‘yan kasuwa damar sayan mai kai tsaye daga matatar.
Shugaban kungiyar ta IPMAN, Abubakar Maigandi, ya bayyana haka a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce an san cewa a halin yanzu kamfanin NNPC shi ne kadai ke da alhakin samar da mai daga matatar ta Dangote, ‘yan kungiyar IPMAN na ci gaba da tattauna wa da wa'yanda alhakin sayar da man ke a hannun su.
Ya ce a halin yanzu kamfanin NNPCPL ya bukaci su aika da tankunan dakon man fetur zuwa matatar mai domin basu kaya, kuma sun bi wannan tsarin tare da mika takardun su ga jami'an matatar.
Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, ba za su iya sayen mai kai tsaye daga Dangote ba amma suna saye daga NNPCPL.
Sai dai ya ce ana ci gaba da tattauna wa dan saukaka wa wa'yanda ke dakon man daga hannun NNPCL.