![]() |
Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar |
Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro a fadin kasa baki daya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Gwamna Uba Sani ziyarar ban girma a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna a wani rangadin da ya ke yi a shiyyar Arewa maso Yamma.
Ziyarar dai na da nufin kammala shirye-shiryen kaddamar da shirin ‘Operation Fansan Yamma' domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.