Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rage kashi 55 na farashin shinkafa da sauran kayayyakin masarufi da aka sawo wa al’ummar jihar kan kudi naira biliyan 14.
Gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da hakan Litinin dinnan, lokacin kaddamar da kwamitocin sa ido na jihar da na kananan hukumomi kan siyar da kayan abincin bisa farashi mai rahusa.
A cewar Gwamna Aliyu, matakin na da nufin rage tasirin wahalhalun da ake fuskanta a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur a kasar.