Gwamnatin Nijeriya ba za ta ba da tallafin aikin hajjin 2025 ba - NAHCON


Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Sanarwar ta ce a aikin Hajjin shekarar 2025, ba za a samu rangwame daga gwamnati kan biyan kudin aikin hajjin ga maniyyata ba a karkashin ma’aikatan aikin Hajji ko na masu zaman kansu.

Hakan na nufin idan har aka cigaba da sayar da Dala daya kan Naira 1,650, kowane mahajjaci zai biya kusan Naira miliyan 10 na kudin aikin hajji yayin da ake sa ran maniyyata su biya akalla Dala 6,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp